Za’a yiwa Samari Biyu Bulala 12 kowannensu Bayan Kama su da Tabar Wiwi a Kano

0
102

Wata kotun Majistiri dake Kano a yau Talata ta yanke hukuncin yin bulala 12 ga mutane biyu, Mohammad Sani mai shekaru 24 da Saddam Ali mai shekaru 27 bisa ta’ammali da tabar wiwi da sauron kwayoyi.

Mutanen biyu an gurfanar da su gaban kotun bisa mallakar tabar wiwi da sauran kwayoyin bugarwa.

Mai shari’a Faruk Ibrahim ya samu mutanen da laifi ne bayan sun amsa laifunsu na mallakar muggan kwayoyi.

Mai shari’a ya bada umarnin a yi musu bulala 12 kowannensu bayan sun nuna nadamarsu.

Tun da farko, mai gabatar da kara, Muhammas Bichi, ya shaidawa kotun cewa, masu laifin sun aikata laifun da aka tuhumesu dashi ne ranar 21 ga watan Disamba da karfe 9 na dare a unguwar Fagge Plaza dake Kano.

Ya ce yan sanda sun kama su da wiwi da kwayoyi wanda ya ce laifin ya saba da dokar Penal Code sashi na 403.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here