Tsohon Shugaban Hukumar Tsaro ta Farin Kaya ya Bukaci Buhari Ya Sauke Manyan Hafsoshin Tsaro

0
133

Tsohon darakra Janar na hukumar tsaro ta farin kaya(DSS), Mike Ejiofor, ya bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada mamaki a shekarar 2021 ta hanyar sauke dukkan manyan hafsoshin tsaron kasarnan tare da nada sababbi don dakile matsalolin tsaro da ake fuskanta.

Yayin da yake tattaunawa da gidan talabijin na Channel, tsohon shugaban hukumar tsaron ta farin kaya ya ce za ta ga ci gaba a yaki da ta’addanci, ayyukan yan bindiga, sace mutane da sauran laifuka, dole Buhari ya sauya dabarunsa, kayan aiki da kuma dadaddun shugabannin hukumomin tsaro.

“Ina tsammanin shugaban kasa zai bai wa yan Najeriya mamaki; Sauya manyan hafsoshin tsaro. Yan Najeriya da halayarsu ga hukumomin tsaro shi ma zai sauya”, inji Ejiofor.

” Ina tunanin sauya dabaru, kayan aiki, halayya, manyan hafsoshin tsaro, zamu samu nasara, ina da kwarin gwiwa kan hakan sosai”, inji shi.

 

Jama’a da dama dai na ta kiraye-kiraye ga shugaban kasa kan ya sauya manyan hafsoshin tsaro ciki har da majalisun dokokin Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here