Mun Fi Mayar da Hankali Kan Wayar da Kan Al’umma Wajen Dakile Yaɗuwar Korona a Kano – NOA

0
194

 

Daga Nusaiba Abdul’aziz Muhammad

Hukumar da ke wayar dakan Al’umma ta kasa reshen jihar kano (NOA) ta nemi Hadin kan Al’umma da su ba ta goyon baya wajen ganin an kiyaye ka’idojin Hana bazuwar annobar Korona musamman a jihar Kano.

Daraktan Hukumar a jihar kano, Alhaji Lawan Haruna Danrokal shi ne ya Bayyana hakan sa’ilin da Suke Ganawa da wakiliyar Jaridar PRIME TIME NEWS.

Alhaji Lawan ya ce ya zuwa wannan Lokaci Abunda suka fi Mayar da Hankali akansa a wannnan lokaci shine wayar da kai kan fadakar da Mutane yanda zasu kare kansu daga kamuwa da cutar Korona duba da cewar wannan shine Karo na biyu na Sake Bullar ta a Kasashen Duniya ciki Kuwa Hadda kasar Najeriya.

Daraktan ya ce kama ta yayi ace Al’ummar Jihar Kano Sun kasance masu Taka tsantsan ta hanyar Daukan Matakan kariya daga Ita wannan Annobar ta Hanyar Amfani da Amawali, da kuma sinadarin tsaftace Hannu tare da Bayar da tazara dakuma bin Duk wasu Matakan Da Masana Kiwon lafiya suke Bayarwa.

A karshe ne Alhaji lawan Haruna yace Za su yi Duk mai yuwuwa wajen Ganin sun Hada kai da Masarautu 5 dake Fadin jihar nan da masu Rike da Masarautun gargajiya hadi da Limamai Dan Ganin an Kaucewa Yaduwar wannan Annoba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here