An Kashe Ƴan Jarida 50 Tare da Ɗaure 387 a Shekarar 2020 – Rahoto

0
161

Kungiyar yan Jaridu ta Duniya wato Reporters without Borders a yau Talata ta ce an kashe yan Jarida 50 da ma’aikatan kafafen yada labarai a sakamakon aikinsu a shekarar 2020 inda hakan ya faru a yawancin kasashen da ake fama da tashe-tashen hankula.

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ce adadin ya nuna karin yawaitar kashe yan jaridar da ke binciken kwakwaf kan laifuka, cin hanci da rashawa da fannin da ya shafi muhalli.

Kashi 84 na wadanda aka kashe a wannan shekarar ya na da alaka da ayyukansu idan aka kwatanta da kashi 63 a shekarar 2019 kamar yadda rahoton kungiyar na shekara ya bayyana.

Kasar Mexico ce tafi zama mafi hadari inda aka kashe yan Jarida 8.

“Alakar dake tsakanin masu safar muggan kwayoyi da yan siyasa ce ta sa, yan jaridar da ke bayyana irin wannan harkalla ko makamancinsa su ke  ci gaba da zama wadanda makasa su ke hari”, inji rahotan.

Sannan kungiyar ta ce har yanzu ba’a hukunta masu kashe yan Jarida ba a kasar ta Mexico.

An kashe yan Jarida 5 a kasar Afghanistan, kungiyar ta ce ana samun yawaitar kai hari kan yan Jarida a yan watannin nan duk da ana ci gaba da tattaunawa tsakanin kungiyar Taliban da Gwamnati.

Kungiyar ta kuma bayyana kashe Ruholla Zam da Kasar Iran ta yi a watan Disamba a matsayin wata alama da ke nuna cewa kasar da aka fi kashe yan Jarida a hukumance.

Sannan kungiyar ta soki kasashen Amurka da Faransa kan yadda aka ci zarafin yan Jarida yayin kawo rahotan zanga-zanga.

Ta zayyano yan Jarida 387 da aka daure, wanda ta kira a matsayin ” adadi mafi yawa a tarihi”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here