Wasu da ake Zargin Ƴan Daba ne Sun Kashe wani Mutum a Unguwar Kurna Dake Kano

0
217

Wasu gungun mutane dauke da makamai, da ake zargin masu aikata kisa ne, a safiyar yau Litinin sun shiga unguwar Kurna tare da kashe wani mutum mai suna Idris Salisu Goma.

Goma, dai ya na aiki da kamfanin samar da takin zamani a karamar hukumar Ungoggo dake jihar Kano.

Jaridar Sahelian Times ta rawaito cewa, yan daban sun hadu da mutumin ne a gurin Sallah tare da kai masa hari da wukake.

Wata majiya ta bayyana cewa, “mun yi kokarin kai shi asibitin Murtala Muhammad, sai dai jini ya zuba dayawa a jikinsa. Ya rasu kafin mu isa Asibitin.”

Ya kara da cewa, “a yan kwanakin nan, yan daba na addabar al’ummar yankin”.

Ba wani bayani da ya bayyana kan dalilin kai harin. Kodayake wata majiya ta shaidawa Sahelian Times cewa watakil dakko hayar makasan aka yi.

A yayin da ake hada wannan rahotan, jaridar ta Sahelian Times ba ta samun damar zantawa da kakakin rundunar yan sanda ta Kano ba, bayan gaza daukar wayar da aka yi mi shi.

Kano dai na fuskantar matsalar masu kwacen waya da yan sara suka da ake kira yan Daba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here