Bola Tinubu Ya aika Sakon Ta’aziyya Ga Kwankwaso Bisa Rasuwar Mahaifinsa

0
109

Jagoran jam’iyyar APC na kasa, Bola Tinubu, a yau Litinin ya mika sakon gaisuwa ga tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso bisa rasuwar mahaifinsa Musa Saleh Kwankwaso.

Musa Saleh ya rasu ne a safiyar ranar Juma’a.

A wata sanarwa da Tinubu ya fitar mai taken, ‘Jajantawa ga Kwankwaso bisa rasuwar mahaifinsa’, ya bayyana marigayi Musa Saleh a matsayin mai riko da addini kuma hakimi a karamar hukimar Madobi wanda ya samar da shugabanci abin koyi”.

Ya kara da cewa”Rasuwar mahaifanmu abin bakin ciki ne sosai. Ko da kuwa sun kai shekaru da dama. Baza mu taba so su rasu ba.

“Na kuma san yadda kuke da kusanci da Baba da irin tasirin da yake a kanka.

“Dole mu gode Allah, Baba ya yi rayuwa cikin shekaru masu muhimmanci, ya shugabanci al’ummarsa da hidimatawa Najeriya”.

” Muna Farin ciki Baba ya bar ‘ya’ya masu daraja da suka hada da kai wanda kullum kake yin kokarin ka hidimtawa jiha da kasa a bangarori da dama.

“Allah Ya yi rahma gare shi, ya gafarta masa, ya sa aljannah makoma, ” inji Bola Tinubu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here