Jonathan Ya aika Sakon Ta’aziyya Ga Kwankwaso Bisa Rasuwar Mahaifinsa

0
147

Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya mika sakon ta’aziyya ga tsohon gwamnan jihar Kano, sanata Rabi’u Musa Kwankwaso bisa rasuwar mahaifinsa, Alhaji Musa Saleh Kwankwaso.

A wani sakon ta’aziyya da ya fitar a jiya Juma’a ta hannun mai taimaka masa na musamman, Ikechukwu Eze, Tsohon shugaban kasar ya bayyana mahaifin na Kwankwaso a matsayin mutum mai gaskiya kuma shugaba ga al’umma.

Jonathan ya kuma yi addu’ar Allah ya sa aljanna makomarsa.

“Ina mika sakon ta’aziyya ga Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da dukkan iyalan Kwankwaao bisa rasuwar mahaifinsu, Alhaji Musa Saleh Kwankwaso, wanda ya rasu ya na da shekaru 93.

” Marigay Musa Saleh Kwankwaso babban mutane kuma shugaban al’umma wanda hikimarsa ta amfani al’ummar Kano gabadaya.

“Za’a dinga tunashi ga wadanda su ka san shi na kusa bisa nagarta da iya shugabanci.

“Allah ya bawa iyalan Kwankwaso hakuri, Allah yasa aljanna makomarsa.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here