Hadiza Gabon Ta Ba wa Tsohon da ya ce ya na sonta da Aure Kyautar Dubu Dari 200

0
166

Shahararriyar jarumar masana’antar shirya fina-finai ta Kannywood, Hadiza Gabon, ta bada kyautar kudi Naira Dubu 200 ga wani Dattijo mai suna Malam Charki, wanda ya fito a wani bidiyo da ya yadu a kafafen sadarwa na zamani inda ya bayyana cewa yana sonta da aure.

Anga  Malam Charki a wani Bidiyon daban yana bayyana farin cikinsa ga Jarumar, kuma ya sauya matsayarsa daga sonta zuwa matsayin mahaifi gareta.

“Hajiya Hadiza, Allah ya biyaki abinda kika yi min.Kamar yadda kike ce, yanzu na karbi matsayin uba a gareki. Allah ya kaimu bikinki tare dani a matsayin uba”, Cewar Charki wanda ke murmushi da farin ciki.

A bidiyon farko dai, an ga Mallam Charki na neman Auren Jarumar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here