Babu Wani Ɗan Nijeriya Da zai Tsallake Allurar Rigakafin Korona – Ahmad Lawan

0
600

Jaridar Leardership A Yau ta wallafa labarin cewa,  shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan, ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa babu wani dan kasar da za a sauya shi wajen rarrabawa da kuma yin allurar rigakafin cutar korona a lokacin da rigakafin ya iso kasar.

Tuni bangaren zartarwa na gwamnati ta gabatar da kudirin Naira biliyan 400 a gaban Majalisar dokoki ta kasa da nufin sayen alluran rigakafin da za a yi kyauta ga ‘yan Nijeriya.

 

Lawan, a cikin sakonsa na Kirsimeti a ranar Alhamis, ya ce, “Majalisar dokoki ta kasa tare da tuntubar hukumomin da abin ya shafa za su tabbatar da kwazo wajen sayowa da rarraba maganin rigakafin korona lokacin da ya samu.”

Ya ce, “Wannan zai tabbatar da cewa dukkan ‘yan Najeriya sun samu damar yin allurar rigakafin kwayar cutar mai taurin kai.”

Lawan, da abokan aikin sa a dakin taro na sama, a cikin bayanan su daban, sun kuma bukaci ‘yan Nijeriya, musamman Kiristoci da su kiyaye ka’idojin kariya daga cutar yayin da suke murnar haihuwar Yesu.

Sanatocin a sakonninsu daban-daban, sun bukaci ‘yan Nijeriya da su jure halin da ake ciki domin annobar za ta zama tarihi.

Lawan, a cikin wata sanarwa daga mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai, Ola Awoniyi, ya bayyana cewa, bikin na bana ya zo ne a daidai lokacin da duniya ke yakar sake barkewar cutar korona.

Ya ce, annobar ta tilastawa kasashe da dama samar da ka’idoji na kare lafiya a daidai lokacin da al’ada mutane ke taruwa don raba soyayya a bikin haihuwar Yesu.

Lawan, duk da haka, ya nuna kwarin gwiwarsa cewa juriya da halaye masu kyau na ‘yan Nijeriya ba zai taimaka wa kasar nan kawai ba wajen shawo kan kalubalen. Ya ce, bin ka’idojin da ba na magunguna ba zai tabbatar da cewa matsalolinsu ba za su dakatar da bikin murnar Kirsimeti a cikin kasar ba.

Ya kara da cewa, “Ina yin biki tare da Kiristoci masu aminci kuma ina umartar mu duka da mu tuna da mahimmancin Bikin. Ganin yadda lamarin ya faru a karo na biyu na yaduwar kwayar cutar, ya kamata mu kiyaye kuma mu cika ka’idojin da ba na magunguna ba da hukumomi suka sanya, ” kamar yadda jaridar ta Leardership A Yau ta wallafa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here