Hotuna: Yadda Dubban Al’umma Su ka Halarci Jana’izar Mahaifin Kwankwaso

0
283
Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso a wajen Jana'izar Mahaifinsa

An binne gawar marigayi Alhaji Musa Sale Kwankwaso,Majidadin Kano kuma mahaifin Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso bayan sallar Janazah da Malam Aminu Daurawa ya Jagoranta.

 

Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso a wajen Jana’izar Mahaifinsa

Dubban al’ummar musulmai ne suka halarci jana’izar wacce aka yi ta a Miller Road gidan tsohon gwamnan Kano Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.

Dubban Al’umman ne su ka halarci Jana’izar

Wadanda su ka halarci jana’izar sun hada da, tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, Sanata Rufa’i Hanga, Kawu Sulaiman, Murtala Sule Garo da Musa Iliayasu Kwankwaso.

Yayin da ake kaiwa Sanata Kwankwaso ziyarar ta’aziyya

Sheikh Daurawa ya yi addu’ar Allah ya jikansa.

Musa Saleh Kwankwaso ya rasu ne a safiyar Juma’a ya na da shekaru 93 bayan gajeriyar rashin lafiya.


Ya rasu ya bar mata 2 da ‘ya’ya 19 da jikoki da dama.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here