Ganduje Ya Aika da Sakon Ta’aziyyar Rasuwar Mahaifin Kwankwaso

0
183

Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje ya ce cikin jimami ya samu labarin rasuwar Makaman Karaye hakimin Madobi, Alhaji Musa Saleh Kwankwaso, wanda ya rasu da safiyar yau Juma’a ya na da shekaru 93.

A wata sanarwa mai dauke da sa hannun kwamishinan yada labarai, Malam Muhammad Garba, gwamnan wanda ya tafi ziyara ta musamman zuwa kasar Dubai a jiya Alhamis, ya bayyana cewa Alhaji Musa Saleh, za’a dinga tunawa tare da girmama shi bisa gogewarsa da hikimarsa a matsayin mai rike da sarautar gargajiya.

“Amadadina, iyalina, gwamnati da jama’ar Kano, muna mika sakon ta’azziya ga Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, Masarautar Karaye da dukkan al’ummar da yake mulka”.

Gwamna Ganduje ya ce Alhaji Musa Kwankwaso ba wai kadai yana jagorantar Al’ummarsa ba ne, har ma d Kano da Najeriya gabadaya.

Ya yi addu’ar Allah sanya Aljannah Makomarsa tare da ba wa iyalansa hakurin jure rashinsa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here