Abba Gida-Gida Ya yi Ta’aziyya Ga Kwankwaso Bisa Rasuwar Mahaifinsa

0
483

Dan takarar gwamnan jihar Kano a tutar jam’iyyar APC a zaben shekerar 2019, Injiniya Abba Kabir Yusif ya mika sakon ta’aziyya ga tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso bisa rasuwar mahaifinsa Majidadin Kano, Alhaji Musa Saleh Kwankwaso.

A wata sanarwa mai dauke da sa hannunsa, Abba ya bayyana marigayi Majidadin Kano a matsayin mutum mai kyawun hali tare da daraja wanda ya shafe tsawon rayuwarsa wajen hidimtawa al’umma.

“Innalillahi Wa Inna Ilahirrajiun, cikin rashin jin dadi naji labari mara dadi na rashin mahaifinmu, ina son mika sakon ta’aziyya ta ga maigidan mu jagoranmu Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, iyalansa da al’ummar jihar Kano”.

Ina kira da masu zuwa ta’aziyya da su bi ka’idojin kariya daga cutar Korona yayin jana’izar mamacin da za’a yi insha Allah yau da karfe 3 na Rana a Millwr Road”.

Sannan ya yi addu’ar Allah ya sanya Aljanna makomar marigayi, Alhaji Musa Saleh Kwankwaso.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here