2023: APC Za ta Iya Faduwa Zabe a Jihar Jigawa – Gwamna Badaru

0
208

Gwamnan jihar Jigawa, Muhammadu Badaru, ya ce jam’iyyar APC za ta iya faduwa zabe a jihar, a zaben shekarar 2023 idan ba a kawo karshen rikicin da jam’iyyar ke fama dashi ba.

Yayin da yake jawabi a wajen rantsar da shugabannin riko na jam’iyyar APC a birnin Dutse yau Juma’a, Badaru wanda ya kasance gwamna karo biyu karkashin jam’iyyar ya ce, Bazai daga kafa ga duk dan jam’iyyar da ke alaqa da wani tsagi na rabuwar kai a jam’iyyar a Jihar.

Kaddamar da kwamitin na zuwa ne bayan cire Habibu Sara daga mukamin shugabancin jam’iyyar a Jihar.

An zargi Habibu Sara da yin biyayya ga Sabo Nakudu, Sanata mai wakiktar Jigawa ta tsakiya.

Gwamnan ya nemi kwamitin rikon da ya jajiece wajen hadin kan jam’iyyar a jihar.

“Zan ci gaba da sanya idanu don lura da wasu daga cikinku dake ganawa da wasu kungiyoyin tsagin jam’iyya, na yi hakuri daku sosai. Bazan kara daga kafa ba nan gaba”,inji shi.

“Abin sha’awa ne yadda jihar Barno da Yobe APC ke zaune lafiya.Jigawa ma haka, akwai bukatar mu dau darasi wanda hakan zai sa mu ci gaba da jagoranci.

“Idan mu ka bar ra’ayin kashin kanmu ya rinjayi ra’ayinmu gabadaya, ina tabbatar muku zamu fadi zabe.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here