Za mu yi Gagarumar Zanga-Zanga Matukar ASUU ta Kara Shiga Yajin Aiki – NANS

0
152

Kungiyar Daliban Najeriya ta ce yan kungiyar za su tsunduma gagarumar zanga-zanga matulakar kungiyar ASUU ta dawo yajin aikin da ta janye.

Shugaban kungiyar Daliban ta NANS, Sunday Asefon, ne ya bayyana hakan yayin tattaunawa da jaridar The PUNCH a yau Alhamis.

Ya ce, abun kunya ne da ban haushi ga ASUU ace ta kara yin barazanar yin wani yajin aikin bayan bata watanni 9 na karatun daliban Najeriya.

Asefon ya ce “Cin fuska ne gare mu, ASUU ta ce tana janye yajin aiki bisa sharadi. Idan su ka dawo da yajin aikin, zamu fito kan tituna. Idan wannanne yaren da kadai suke fahimta, zamu yi shi gare su”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here