Mun Shirya Tunkarar Duk Wata Barazana da Cin Zarafi daga APC, PDP ta yi Martani Kan Kalaman Abdullahi Abbas

0
135

Babban Jam’iyyar adawa ta PDP ta mayar da martani kan kalaman da shugaban kwamitin riko na jam’iyyar APC, Abdullahi Abbas ya yi na cewa “abinda ya faru a shekarar 2019 shi za su maimaita a zaben 2023.

A sanarwar da Jam’iyyar reshen jihar ta fitar, ta hannun kakakin jam’iyyar, Bashir Sanata, wacce ke dauke da sa hannun shugaban jam’iyyar, Shehu Wada Sagagi kuma ta aikowa da jaridar PRIME TIME NEWS ta ce kalaman na Abdullahi Abbas sun nuna karara cewa APC ba jam’iyyar Dimukuradiyya ba ce.

Sanarwar ta ce “bisa kalaman da Abdullahi Abbas ya yi, za’a lura cewa:

“Zaben shekarar 2019 wanda hanyar Dimukuradiyya ne ya tabbatar da Abba K. Yusif a matsayin wanda ya lashe zaben da gagarumin rinjaye wanda kuma aka yi fashinsa da abinda ya saba doka wai shi Inconclusive.

“Rigingimu da aka yi yayin zaben na biyu sun nuna APC ce ta shirya shi.

“Shirin APC shi ne ta kara yin abinda ta yi a zaben 2019 na rigingimu kuma baza ta shiga zaben da za’a gudnar cikin kwanciyar hankali ba”, inji sanarwar.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa jam’iyyar a shirye ta ke wajen tunkarar da wata barazana ko cin zarafi daga jam’iyyar APC.

“Mun yi cikakken shirin tunkara da yin maganin duk wata barazana, hari(na gaba da gaba, ko na fatar baki), cin zarafi da APC za ta yi da gwamnatinta don kare hakkinmu, kuri’un mu da nasararmu a kowanne lokaci idan bukatar hakan ta taso”.

Daga karshe jam’iyyar ta yi kira ga kwamishinan yan sandan jihar Kano, Daraktan rundunar tsaron farin kaya ta DSS da sauran hukumomin tsaro da su lura sosai kan kamalan na Abdullahi Abbas.

Sannan Jam’iyyar ta PDP din ta yi kira ga bangaren shari’a, da hukumar zabe da su dau darasi kan abinda ya bayyana dangane da zaben shekarar 2019 da kuma shirin jam’iyyar APC a shekarar 2023.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here