Makarantar Bayar da Horo Kan Dabarun Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta fara Aiki a Kano

0
155

Gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya kaddamar da makarantar bayar da horo kan yaki da cin hanci da rashawa ranar 9 ga watan Disamba, 2020 bayan kafata da aka yi a watan Yuli na shekarar 2020.

Mataimakin gwamman jihar Kano, Dr. Nasiru Yusif Gawuna shi ne ya wakilcin gwamnan yayin bikin kaddamar da makarantar.

Makarantar na da damar horar da ma’aikatan hukumar yaki da cin hanci da rashawa da karbar korafe-korafe ta jihar Kano a guraren ayyukansu da kuma kara mu su ilimi don tabbatar da gaskiya da yin komai a bude.

Samun nasarar kafa wannan makarantar horar da dabarun yaki da cin hanci da rashawar ya samu ne bisa kokarin shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa da karbar korafe-korafe ta jihar Kano, Barista Muhyi Magaji.

Ma’aikata dai daga ma’aikatar shari’a da na hukumar sun samu horo kan bangarori da dama.

Makarantar na shirin samar da sabon tsari a sabuwar shekara inda take shirin horar da wasu ma’aikata daga hukumomin gwammati.

Makarantar a shirye ta ke wajen bayar da horo kan tafikar da lamura cikin gaskiya da yin komai a bude, bincike, samar da masalaha da wasu bangarori da dama ga hukumomin gwamnati da na masu zaman kansu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here