Yadda Siyasar Kano Ta Ɗau Zafi Tun Kafin Kakar zaɓen 2023

0
451

A yayin da shekarar 2020 ke yi mana bankwana inda muke daf da shiga shekarar 2021, siyasar Kano ta dau dumi tun kafin shiga kakar zabe ta 2023.

Tun karatowar zaben kananan hukumomi a jihar ne a ka fara jifan juna da zafafan kalamai tsakanin manyan jam’iyyun Adawa a jihar wato APC mai mulki da PDP.

Haka nan kuma ga rikicin cikin gida da ya dabaibaye jam’iyyun.

Jam’iyyar PDP, babbar mai hamayya a jihar ta na fama da rikicin cikin gida tsakanin bangaren Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da na Aminu Wali wanda kowanne ke ikirarin shi ne ke rike da jam’iyyar, ko dayake uwar jam’iyyar ta kasa ta tabbatar da shugabancin jam’iyyar tsagin da ke biyayya ga Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso abinda ke nuni da cewa, Kwankwaso ne ke da karfin Iko a jam’iyyar.

Jam’iyyar ta PDP dai a kwanakin baya ta ce ba za ta shiga zaben kananan hukumomi da za’ayi a jihar ba inda ta ce baza ayi mata adalci ba.

Sai dai jam’iyyar APC din ta bayyana cewa, yan Kwankwasiyyar na tsoron shan kayi ne shi yasa taki shiga zaben.

Kalaman da tsohon gwamnan Kano, kuma jagoran darikar Kwankwasiyya, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya yi na cewa “Shekarar 2023 za ta kasance ko a mutu ko ayi rai” sun tada hazo inda suka tunzura shugaban jam’iyyar APC na Kano, Abdullahi Abbas inda ya mayar da zazzafan martani.

Yayin rantsar da shugabbanin riko na Jam’iyyar APC a Kano an jiyo Abdullahi Abbas na ikirarin cewa “Za su murde zabe kuma ba abin da aka isa ayi”, kalaman da suka kara zafafa al’amuran siyasa a jihar.

A gefe guda kuma, an hango wani faifan Bidiyo na dan majalisar tarayya mai wakiltar karamar hukumar Birni, Sha’aban Sharada na caccakar gwamnan jihar Kano kan yadda yake siyar da kadarorin gwamnati wanda hakan ke nuni da tsamin alaka tsakaninsa da shugabancin jam’iyyar na Kano.

Sai dai, tuni wasu jama’ar Kano su ka fara nuna fargabar su kan yadda yanayin siyasa ka iya kasancewa a shekarar 2023.

Abin jira a gani dai shi ne yadda al’amura za su kasance musamman idan aka tunkari kakar zabe ta shekarar 2023.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here