Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Garin Minjibir tare da Sace Wani Ɗan Kasuwa

0
217

Yan bindiga da ake zargin masu sace mutane ne sun sace wani dan kasuwa mai suna, Alhaji Abdullahi Kalos, unguwar yamma, a karamar hukumar Minjibir dake jihar Kano.

Yan bindigar sun kuma kona motar yan sanda yayin kai harin.

Jaridar Sahelian Times ta rawaito cewa, yan bindigar sun dira cikin garin ne tare da manyan bindigu wajen karfe 2 na daren Laraba.

“Yan bindigar sun fara harbi a sama kafin su sace shi”, inji wani mazaunin yankin.

” Bayan DPO ya samu labari sai ya tura jami’ansa, sai dai yan bindigar sun bar wajen kafin yan sandan su zo”.

Yayin da ake hada wannan rahotan, ba’ a samu wayar kakakin rundunar yan sanda, DSP Abdullahi Haruna ba don jin ba’asin rundunar kamar yadda Jaridar ta Sahelian Times ta rawaito.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here