Sakamakon Gwaji Ya nuna Ba na Dauke da Cutar Korona – Tambuwal

0
121

Gwamman Jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal ya ce gwajin da aka yi masa ya nuna cewa baya dauke da cutar Korona.

A sanarwar da gwammnan ya fitar ya ce “Idan za’a iya tunawa dai na killace kaina bisa alaka da nayi da wanda ya kamu da cutar Korona.

” yayin da na killace kaina, na dinga sa wa ana yimin gwaji daga hukumomin da abun ya shafa don sanin ko na kamu da cutar ko a’a.

“Cikin godiyar Allah, ina mai sanar da al’umma musamman jama’ar Sokoto, cewa sakamakon gwajin da aka yi min da dama sun nuna bana dauke da cutar Koroma”.

Tambuwal ya kuma godewa Mataimakinsa, Hon Munir Dan’iya, Walin Sokoto, bisa rike mulkin jihar yayin da gwamnan ya killace kansa, sanan gwamnan ya godewa, mai alfarma Sarkin Musulmai bisa kulawarsa gare shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here