Gwamnatin Tarayya ta ce da Yuwuwar ta Sake Rufe Iyakokin Najeriya

0
123
Shugaban Kasa Buhari Ke Jawabi Gaban Daliban yau juma'a a Katsina

Gwamnatin tarayya a yau Talata ta ce da yuwuwar ta sake kulle iyakokin kasarnan.

Rufe iyakokin an yi shi ne don hana shigowa da kananan makamai.

Mai taimakawa shugaban kasa Buhari kan kafafen yada labarai, Malam Garba Shehu ne ya bayyana hakan yayin tattaunawa da gidan Talabijin na Channel.

Garba Shehu ya ce gwamnatin tarayya har yanzu na karantar yadda lamura suke a iyakokin kan tudu na kasarnan, inda ya kara da cewa, idan aka ci gaba da samun matsaloli to gwamnati ba ta da wani zabi face ta sake rufe iyakokin.

Ya kuma tirje kan cewa kasashe makotan Najeriya na ba wa Najeriya wuya wajen yaki da yaduwar kananan makamai.”wannan ne dalilin da ya sa shugaban kasa ya bada umarnin rufe iyakokim”, inji shi.

“Ana ci gaba da tattaunawa tsakanin Najeriya da kasashe makwabta, don lalubo hanyar da za’a dakile yaduwar makamai, fasa kwauri, safarar mata. Amma abin da wuta”, inji shi.

“Hakan ne ya tilasta shugaban kasa rufe iyakokin”, Inji Garba Shehu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here