A Yau Buhari Zai Gana da Kwamitin Yaki da Korona yayin da ake Fargabar Sanya Dokar Kulle

0
135

Sashin Hausa na BBC ya wallafa labarin  cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari zai gana da kwamitinsa mai yaki da annobar cutar korona anjima a yau Talata, a cewar fadar shugaban.

A jiya Litinin ne kwamitin karkashin jagorancin Boss Mustapha, sakataren gwamnatin tarayya, ya sake bayar da umarnin wasu sabbin matakai na yaki da cutar sakamakon yaduwarta a karo na biyu.

Duk da cewa babu tabbacin abin da za su tattauna, kwamitin zai gabatar wa da Buhari shawarwari wadanda ka iya kai wa ga fito da wasu sabbin matakan irin na dokar kulle.

Daga cikin umarnin da kwamitin ya bayar na jiya, ma’aikatan gwamnati daga mataki na 12 zuwa ƙasa za su yi aiki daga gida har nan da mako biyar.

Sannan duka makarantu a faɗin ƙasar za su kasance a rufe har zuwa watan Janairun 2021.

Kwamitin ya bayyana cewa gidajen rawa da wuraren shan barasa da kuma wuraren motsa jiki za su ci gaba da zama a rufe a ƙasar.

Sannan kuma kwamitin ya bayar da umarnin rufe gidajen abinci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here