2023: “Zamu Murɗe Zaɓe kamar Yadda muka yi a 2019 Kuma Ba abin da aka isa ayi” – Abdullahi Abbas

0
275

Jam’iyyar APC reshen jihar Kano a yau Talata ta bayyana zafafan kalamai kan jam’iyyun adawa a jihar inda ta ce a shirye ta ke da yin fada da jam’iyyun Adawan.

Shugaban jam’iyyar a Kano, Abdullahi Abbas ya yi gargadin cewa, jam’iyyar baza ta amince da kowacce irin adawa a jihar ba, inda ya umarci yan jam’iyyar da su tunkari yan hamayya a kowanne irin mataki.

Yayin da yake jawabi ga yan jam’iyyar a gidan gwamnatin jihar Yayin rantsar da shugabbanin riko na jam’iyyar na kananan hukumomi 44, Abdullahi Abbas ya kuma umarci yan jam’iyyar APC a jihar kar su ji saurara wajen kai hari ga magoya bayan tsohon gwamnan Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso.

Abdullahi Abbas ya kuma bayyana cewa, zaben shekarar 2023 zai kasance yadda jam’iyyar ke so, inda ya ce ” Baza mu yarda a yi zabe yadda yakamata ba, sai dai za a mai-mai ta zaben inconclusive kamar yadda aka yi a 2019, za mu murde zaben kamar yadda muka yi a Gama”.

“Lokacin yin sahihin zabe a Kano ya wuce. Za mu tabbatar da mai-maituwar zaben inconclusive a shekarar 2023. APC za ta ci gaba da rike gwamnati tun daga sama har kasa.

“Ina kira a gare ku kar ku saurarawa duk wani dan Kwankwasiyya”.

Ya kuma bayyana cewa zai ci gaba da lashe zabe ” Ko da tsiya ko da tsiya-tsiya”.

Abdullahi Abbas ya kuma kara yin kira ga yan jam’iyyar APC da su ci gaba da matsaya yan jam’iyyar PDP ta hanyar shirye-shiryen Rediyo ko gaba da gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here