Yanzu-Yanzu: Za’a Koma Jami’o’i a Watan Janairu – Ngige

0
170

Ministan Kwadago, Chris Ngige ya ce kungiyar malaman jami’o’i ta ASUU za su koma aikin koyarwa a watan Janairu na sabuwar shekara dake kamawa.

Ya ce tattaunawar sulhu tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyar ta ASUU ta kai kashi 98 inda kashi biyu ne ya rage a kammala.

Ya na bayanin hakan ne a yau Litinin jihar Anambra, yayin kaddamar da bayar da tallafin magunguna.

Ngige ya ce “Mun cika kashi 98 na bukatun ASSU. Wasu 5 zuwa 2 ne suka rage.

” Don haka, ina fatan a daren yau, akwai wasu ayyuka da za mu yi. Suma akwai abubuwan da za su da mutanensu.

“Ranar Talata zamu kara haduwa da yamma, ina da yakini za’a kawo karshen yajin aikin a gobe”.

Ministan Ya ce idan suka cimma matsaya a gobe, za’a koma jami’o’i a watan Janairu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here