Yanzu-Yanzu: Gwamnatin Tarayya ta Fitar da Sabbin Matakan Hana Yaɗuwar Korona

0
364

Gwammatin tarayya ta sanya sabbin matakan hana yaduwar cutar Korona a yayin da ake samun yawaitar masu kamuwa da cutar.

Boss Mustapha wanda shi ne shugaban kwamitin kar ta kwana na fadar shugaban kasa kan yaki da annobar Korona, ne ya bayyana hakan a yau Litinin a yayin taron yiwa manema labarai jawabi da kwamitin ke yi a Abuja.

Sabbin matakan sun hada da rufe dukkanin guraren sharholiya, gidajen rawa da gidajen taruka da biki a dukkan jihohin kasarnan.

Sannan an umarci gidajen abinci da su rufe, sai dai ban da wadanda ke samar da abinci ga Hotal, da masu kaiwa gidaje.

Sannan dukkan tarukan biki ko bukukuwan karshen shekara kar a tara mutane sama da 50.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here