Ya Kamata a Ba wa Kowa Damar Mallakar Makami Don Kare Kansa – Sarkin Anka

0
146

Sarkin Anka a jihar Zamfara, Alhaji Attahiru Ahmad, ya roki gwamnatin jihar ta bada dama ga al’ummar jihar da su mallaki makamai don kare kansu daga harin yan bindiga.

Sarkin, wanda ya kai ziyarar jaje ga Sarkin Kaura-Namoda wanda yan bindiga su ka kaiwa hari a makon da ya gabata ya ce “tunda yan bindiga sun ki ajiye makamai, yakamata gwamnati ta ba wa kowa damar rike mukami don kare kai”.

Ya ce, tsarin yin sulhu da gwamna Bello Matawalle ya samar ba zai kawo karshen ayyukan yan bindigar ba a jihar, saboda yan bindigar ba za su taba dena abinda suke ba.

Sarkin, wanda shi ne shugaban majalisar Sarakunan jihar, ya ce ” ba wanda zai iya samar da zaman lafiya ga mutanen da ba su shirya zama lafiya ba da yin sulhu wanda gwamnati ta samar.

“Duk duniya babu wani mutum daya da yafi karfin gwamnati, sai dai idan gwamnati ba ta son gamawa da shi”.

Haka kuma ya bukaci gwamnati ta ba wa jami’an tsaro dama wajen ganin bayan yan bindigar, inda ya ce jami’an tsaro za su iya shawo kan matsalar matukar a ka basu dama da makamai.

Idan za’a iya tunawa dai, An kai hari ga Sarkin Kaura-Namoda, Alhaji Sanusi Muhammad a hanyar Zaria-Gusau ranar Alhamis yayin da yake dawowa jihar daga Abuja inda aka kashe mutane 8 daga tawagarsa.


 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here