Hisbah Ta Kama Ƙaruwai 14 Dake Ɗauke da Cutar Ƙanjamau a Kwanar Gafan Da ke Kano

0
325

Hukumar Hisba ta jihar Kano ta kama samari da mata masu zaman kansu 43 dake yin sana’ar karuwanci da siyar da giya a Kwanar Gafan, dake karamar hukumar Garun Malam a jihar.

Dr. Harun Ibn Syna, kwamandan rundunar Hisba ra jihar Kano wanda ya yi holan wadanda ake zargin a yau Litinin a shelkwatar hukumar ya tabbatar da kama matan.

“Daga cikin mutane 43 da aka kama, 34 mata ne yayin da ragowar kuma maza ne da shekarunsu yake tsakanin 15 da 18.

” Binciken da aka gudanar kan wadanda aka kama din ya nuna cewa takwas daga mazan an same su suna siyar da kwayoyi yayin da aka samu daya da katon 80 na kwalaben giya”, inji Jbn Syna.

Ya ce Mutane 14 suna dauke da cutar HIV, 10 sun san suna dauke da ita yayin da hudu basu sani ba sannan an samu kwaroran roba na maza da mata a kasuwar ta Kwanar Gafan.

Ya ce an kama su ne bisa hadin gwiwar hukumar Hisba da kuma hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi.

Tun da farko, a nasa jawabin, Daraktan hukumar, Dr. Aliyu Kibiya ga bayyana cewa, yawancin wadanda aka kama din yan Kano ne yayin da wasu kuma daga makotan jihohi su ke da suka hada da Adamawa, Anambra, Cross River, Bauchi, Benue, Kaduna, Niger, Gombe da Taraba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here