An Kaddamar Da Shafin Siya da Siyarwar Kayan Miya da Sauran Kayayyaki ta Internet a Kano

0
480

An bude manhajar siya da siyar da kayayyaki na cikin gida da waje anan Kano.

Shafun manhajar mai suna http://www.herb.ng an kaddamar da shi ne a yammacin jiya Lahadi, 21 ga watan Disamba, 2020 a ofishin PRNigeria dake unguwar Kofar Famfo a Kano.

Yayin da yake tattaunawa da jaridar PRIME TIME NEWS jim kadan bayyan kaddamar da shafin, wanda ya kirkiro da shafin, Rabi’u Abdul Aliyu ya ce shafin ya kunshi siya da siyarwa na kayayyakin gargajiya da abubuwan amfani na gida.

“Wannan Platform ne da ya kunshi siya da siyarwa na kayan gargajiya irin namu na gida, mun hada shi ne domin mu samarwa mutanen mu sauki, na yadda za su dinga siya da siyarwar abubuwansu na gargajiya kamar kayan miya, tumatiri, attaruhu, goriba da komai gami da maye-mayen shafawa”.

Sannan ya kara da cewa, duk wanda ya siyi kaya za’a kawo masa kayansa har gida cikin mintuna 20.

Sannan ya kara da cewa, zaka iya siyan kaya ta wayarka, idan an kawo ma gida ka bada kudin kayan.

Tun da farko Rabi’u Abdul Aliyu ya ce abinda ya ja hankalinsu wajen samar da shafin shi ne garin irin wahalar da mutane su ka shiga a lokacin dokar kulle inda ake samun wahala kafin a fita ayi siyayyar kayayyaki.

Shima anasa jawabin, daya daga cikin wadanda suka kirki shafin, Umar Nuhu Abba ya shaidawa Jaridar PRIME TIME NEWS cewa za su yarjejeniya da duk wanda ke son siyan kaya inda za’a iya sauya masa kayan da ya siya idan basu yi masa ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here