2023: Ƴan Siyasa a Kudu Maso Yammacin Ƙasarnan Sun Kaddamar da Takarar Tinubu

0
183

Kungiyar tsofaffin Sanatoci, yan majalisar wakilai da yan siyasa dake jihohin kudu maso yammacin kasar nan sun kaddamar da yakin neman zaben “Tinubu a matsayin shugaban kasa” a zaben shugaban kasa na 2023.

Sun fara yakin neman zaben ne da kai ziyara ga Olabadan na Ibadan, Oba Saliu Adetunji da Alaafin na Oyo O a Lamidi Olayiwola Adeyemi 111 a ranar Litinin da ta gabata.

Kungiyar karkashin jagorancin tsohon Sanata Dsyo Adeyeye sun ce sun hadu ne don tabbatar da yakin kudu maso yamma ya samar da shugaban kasa a shekarar 2023.

Tinubu dai shi ne Jagoran jam’iyyar APC na kasa, kuma yana daga cikin wadanda suka yi ruwa da tsaki wajen ganin Buhari ya zama shugaban Najeriya.

Sai dai ana ganin ya na ta yunkurin ganin ya zama magajin shugaba Buhari a zaben shekarar 2023.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here