Ɗan Shekara 50 Da ke da Ƴaƴa 150 a Faɗin Duniya Ya ce Zai Ci gaba da Ziyarar Matan Da ke Bukatarsa

0
210

 

Fitaccen mai bada tallafin maniyyi na duniya, Joe Donor, wanda ya samu ƴaƴa 150 ta hanyar yiwa mata 10 ciki a  kowacce shekara, ya bayyana cewa har yanzu yana haduwa da matan a fadin duniya duk da bullar annobar Korona.

Jaridar Mirror ta kasa Burtaniya ta rawaito mutumin dan shekara 50 na cewa, Kirismeit ta zo da wuri bayan an fada masa cewa mata uku yan kasar Burtaniya na dauke da cikinsa.

Joe ya yi tafiye-tafiye a fadin duniya da suka hada da Amurka, Agentina, Italy, Singapore da Philippines sai dai yanzu haka yana Ilford, Arewa maso tsakiyar birnin London, inda yake bada tallafin maniyinsa yayin da aka fama da annobar Korona.

Mutumin wanda ya fito daga jihar Vermont ta kasar Amurka, ya ce “Bikin Kirsimeti da yafi kowanne” shi ne gano cewa mata uku yan kasar Burtaniya na shirin haifa masa ya’ya a shekarar 2021, inda ya kara da cewa annobar Korona ba ta sa shi yaja da baya ba.

Dan shekara 50 din, wanda ke bayar da tallafin maniyinsa kuma baya amfani da sunansa na Asali ya na rayuwa a birnin London tsawon watanni uku da suka wuce.

“Taimakawa mata wajen samar da kyautar rayuwa shi ne abinda yafi komai a yanzu. Koyaushe a shirye nake wajen taimakawa mata su samu ‘ya’ya.

“Tun da na iso Burtaniya a watan Satumba na hadu da mata kusan 15. Yawancinsu basu san yin jima’i kamar yadda su ka ce tana haifar da abubuwa da yawa a alaqarsu ta aure yayin da wasu kuma yan madigo ne.

” tun saukata a Burtaniya naje Wales, Hull, Birmimgham, Portsmouth da Kent”, inji shi.

“Ina jin kamar nine wanda nafi kowa nasara a duniya wajen tallafawa mata a lokacin da su ke bukatar taimako. Naji dadin jin cewa mata uku da na hadu da su a Burtaniya sun samu ciki”.

Joe ya ce annobar Korona ba ta sa ya ja da baya ba inda ya bayyana cewa ya yi mata 10 ciki a shekara.

“Ban san hakikanin adadin ba amma a kowacce shekara yana rubanya. Ina amfani da safar rufe hanci da baki yayin yin jima’i don hana yaduwar cutar Korona amma bazai yuwu na bada tazara ba.

“Ina so naga hotunan jarirai yayin da aka haife su yayinda mafi yawancin su suke kama dani. Ba na samun kudi daga bayar da tallafin Maniyyi ga mata, kawai ina jin dadin tallafawa mutane ne, inji shi.

” Ina da ‘ya’ya a fadin duniya, na fara bada tallafin Maniyi a shekarar 2008 inda nake zama uba ga ya’ya 10 kowacce shekara”.

“Zan ci gaba da wannan taimako tsawon lokacin da zan iya wanda zai iya ksancewa lokacin da na shekara 90”, inji shi.

Sannan ya ce ana duba lafiyarsa duk shekara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here