Rundunar Ƴan Sanda Ta Karrama Ƙungiyar Wakilan Kafafen Yaɗa Labarai ta Kano

0
104

Rundunar yan sanda ta kasa, reshen jihar Kano, a jiya Lahadi ta karrama kungiyar wakilan kafafen yada labarai ta Kano karkashin shugabancin Comrde Ibrahim Garba Shu’aib.

Taron karramawar wanda ya samu halartar manyan baki da futattun mutane a Kano a gudanar da shi ne karkashin jagorancin kwamishinan yan sanda na Kano, CP Habu Sani.

“Karramawar an yi ta ne bisa goyan bayan da kuke bawa rundunar yan sanda a cikin shirinta na yan sandan al’umma, wanda ya haifar da babbar nasara”, inji kwamishinan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here