Gwamnan Kwana Ɗaya Ya Saki Ɗaurarru a Jihar Abia

0
231

Wani yaro dan shekara 17 mai suna Nicholas Ogunji wanda ya kasance gwamnan kwana daya a jihar Abia ranar Juma’a ya saki daurarru a gidan gyaran hali na Afarukwu.

Yaron wanda ya halarci makarantar fasaha ta Adventist Ohafia ya saki daurarrun ne a fitarsa ta farko.

“Yanzu haka muna da dan shekara 17, Nicholas Ogunji na Makarantar Sakandiren Adventist Technical, Ohafia a matsayin gwamna na kwana daya”, cewar gwamman jihar Abia, Okezie Ikpeazu a shafinsa na Twitter.

 

“Shi ne na uku a wadanda suka zama gwamanan rana daya a karkashin gwamnatina. Bangaren aikinshi na farko shi ne ziyarar gidan gyaren hali na Afaraukwu inda ya taimaka aka saki wasu daurarru bayan biyan kudin tara”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here