An Ceto Ɗaliban Makarantar Islamiyya da Aka Sace a Katsina

0
166

Rahotannin da jaridar PRIME TIME NEWS ke samu na cewa daliban makarantar Islamiyya da aka yi garkuwa da su a garin Mahuta na karamar hukumar Dandume dake jihar Katsina sun samu shakar yanci.

Daliban da yawansu ya kai 84, rahotanni sun bayyana cewa yan sintiri ne suka kubutar da su.

Yan sintirin sun fafata da yan bindigar da misalin karfe 3 na dare.

Mai magana da yawun rundunar yan sanda reshen jihar Katsina ya tabbatarwa da jaridar PRIME TIME NEWS faruwar lamarin.

Idan za’a iya tunawa dai a ranar Alhamis, dalibai 344 su ka kubuta bayan garkuwar da yan bindiga suka yi da su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here