Yanzu-Yanzu: An Sace Shugaban Ma’aikatan Jihar Edo

0
153

An sace shugaban ma’aikata na jihar Edo, Anthony Okungbowan a birnin Benin.

Wata majiyar tsaro ta bayyana cewa, an sace Okungbowa da yammacin yau Asabar kuma an kai shi wani waje da ba a tabbarar ba, kuma har yanzu wadanda suka sace shi basu tuntubi iyalai ko gwamnatin jihar ba.

Yayin da aka tuntubi kakakin rundunar yan sandan jihar Edo, Chidi Mwabuzor ba a same shi a waya ba.

 

Akwai karin bayani nan gaba…..

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here