Garba Shehu Ya Nemi Afuwa Kan Cewa ‘Ɗalibai 10 Kawai aka Sace a Katsina’

0
209

Mai taimakawa shugaban kan kafafen yada labarai, Malam Garba Shehu ya nemi  afuwa kan bayanin da ya bayar cewa ɗalibai 10 ne kawai aka sace a makarantar sakandaren Kankara a jihar Katsina.

“Ina neman afuwa kan kuskuren bayanai da aka gabatar cewa dalibai 10 ne aka sace a makarantar kimiya ta Kankara.

“Wani ne wanda ya kamata ace ya sani ya bayar da bayanan kan adadin ɗaliban. Adadin kuma yanzu ya ci karo da waɗanda aka gani.

“Don Allah a fahimci cewa bayanan ba an bayar da su ba ne domin rage muhimmancin yanayin da aka shiga,” in ji Garba Shehu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here