Buhari Zai Gana da Ɗaliban Jihar Katsina Da aka Kuɓutar Yau Karfe 3 na Rana

0
240

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai gana da daliban makarantar Sakandiren Kankara da aka kubutar a jihar Katsina yau da karfe 3 na rana.

Mustapha Inuwa, Sakataren gwamnatin jihar Katsina ne ya shaidawa jaridar PRIME TIME NEWS hakan a yau Juma’a.

Inuwa ya fadin hakan ne ta bakin mai magana da yawunsa Abdullahi Yar’adua.

Jaridar PRIME TIME NEWS ta lura da cewa, wasu daga daliban basu da lafiya kuma sun samu ciwo da rashin jin dadi.

Daya daga cikin yaran ya bayyana cewa, sun yi tafiyar sa’o’i 3 a kasa cikin daji kafin su isa maboyar yan bindigar.

Ya ce , kuli-kuli kawai suke bamu”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here