Yanzu-Yanzu: Shugaban Ƙasar Faransa Ya Kamu da Cutar Korona

0
163

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya kamu da cutar korona.

Jami’an ƙasar sun shaida cewa a halin yanzu shugaban zai killace kansa na kwanaki bakwai kuma zai ci gaba da aiki daga gida.

Wata sanarwa da ta fito daga fadar shugaban ƙasar ta bayyana cewa Mista Macron ya yi gwajin na korona bayan jikinsa ya fara nuna alamomin cutar kamar yadda sashin Hausa na BBC ya wallafa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here