
Yanzu haka wakilan gwamnatin tarayya da shugabannin kungiyar ASUU na tattaunawar sirri kan yajin aikin da kungiyar ta shafe watanni ta na yi.
Tattaunawar wacce aka fara da misalin karfe 5:13, ministan kwadago Chris Ngige ya shirya ta bayan dagawa da aka yi har sau biyu.
Idan za’a iya tunawa dai, a tattaunawar da gwamnati ta yi da kungiyar a ranar 27 ga watan Nuwamba ta amince da biyan wasu daga bukatun kungiyar ta ASUU.