Yanzu-Yanzu: An Sako Daliban Da aka Sace a Jihar Katsina

0
396

Sashin Hausa na BBC ya wallafa labarin cewa, gwamnatin jihar Katsina da ke arewacin Najeriya ta ce an samu nasarar karɓo yaran makarantar sakandaren Kankara su 340 a yau Alhamis da daddare.

Sakataren gwamnatin jihar Alhaji Mustapha Inuwa ne ya tabbatar wa da BBC hakan, inda ya ce a yanzu haka ana hanyar kai yaran birnin Katsina daga garin Tsafe na jihar Zamfara da ke maƙwabtaka da ita.

Ya ƙara da cewa a daren yau za a tarbe su a Katsina ƙarƙashin rakiyar jami’an tsaro, sannan a gobe Juma’a Shugaba Buhari zai gana da su a birnin Katsinan.

A ranar Juma’ar da ta gabata ne wasu ƴan bindiga suka dirar wa makarantar kimiyya ta kwana ta maza da ke garin Kankara inda suka yi awon gaba da yara kusan 400.

Kwana hudu bayan haka sai shugaban ƙungiyar Boko Haram Abubakar Shekau ya fitar da saƙo yana ikirarin sace yaran.

Ko a ranar Alhamis da rana ma ƙungiyar Boko Haram ɗin ta fitar da wani bidiyon ɗaliban.

A cikin bidiyon, wanda jaridar intanet ta HumAngle ta fara wallafawa, ya nuna ɗaya daga cikin ɗaliban yana roƙon gwamnatin Najeriya da ta janye sojojin da ta aika domin ceto su yana mai cewa “babu abin da za su iya yi musu wallahi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here