Shehu Wada Sagagi ne Shugaban Jam’iyyar PDP a Kano – Shelkwatar PDP

0
880

Uwar Jam’iyyar PDP ta kasa ta tabbatar da shugabancin jam’iyyar, tsagin dake biyayya ga tsohon gwamnan jihar Kano, Dr. Rabi’u Musa Kwankwaso.

A sanarwar da Sakataren yada labarai na Jam’iyyar Kola Ologbondiya ya fitar a yau Alhamis, ta bayyana Shehu Wada Sagagi a matsayin sabon shugaban jam’iyyar na jihar Kano.

Jam’iyyar ta bayyana cewa, an gudanar da zaben shugabbanin jam’iyyar bisa tsarin doko a ranar 12 ga watan Disamba kuma ba ta karbi wani korafi ba kan yadda a ka gudanar da zaben.

Sanarwar jam’iyyar na zuwa ne bayan da tsagin da Amini Wali ke jagorantar ya sanar da korar Kwankwaso daga jam’iyyar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here