Sace Dalibai: Kungiyoyi na Zanga-Zanga a Jihar Katsina

0
216

Gamayyar kungiyoyin Arewacin Najeriya ta CNG, a yau Alhamis ta fara zanga-zanga don tilastawa gwamnati wajen ceto daruruwan daliban da aka sace daga makarantar Sakandire ta Kankara a jihar Katsina.

Zanga-zangar da shugabbanin kungiyar ke jagoranta, su ne rike da kwale mai dauke da rubutun “Ku dawo mana da yaranmu”, ” Dole gwamnati ta yi magana”, “Muna son ya’yanmu su dawo”.

Sanann masu zanga-zangar su na rera wakar neman a kubutar da daliban.

Yayin da yake jawabi ga manema labarai, shugaban gamayyar kungiyar ya ce ” muna nan ne a yau saboda muna son fadawa gwamnatin tarayya cewa abinda su ke yi bai gamsar ba kuma shugaban kasa ya gaza. Shugaban kasa ya nuna halin ko in kula kan wannan lamarin.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here