Korona: Gwamnatin Kaduna Ta Bada Umarnin Rufe Guraren Taruka da Na Shakatawa

0
62

Gwamnatin jihar Kaduna ta bada umarnin rufe dukkan guraren taruka da shakatawa a fadin jihar a wani bangare na dakile yaduwar annobar Korona zagaye na biyu a jihar.

Gwamnatin jihar ta kuma yi bayanin cewa, duk gidajen cin abinci dole su takaita ayyukansu yayin da masu ababen hawa za su rage yawan daukar fasinjoji da kashi 50 tare da tabbatar da kowanne fasinja ya sanya takunkumin rufe hanci da baki da kuma bada tazara.

Umarnin wanda gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai ya bayar yayin bayani kai tsaye da yayi a kafafen yada labarai na Kaduna ya biyo bayan bayanin da kwamishiniyar lafiya ta Kaduna, Dr. Amina Baloni ta yi na cewa jihar na samu sama da mutane 100 dake kamuwa da cutar Korona a kullum.

El-Rufai ya kuma tabbatarwar da al’ummar jihar cewa, ba matakan da gwamnatin ta dauka ba wai don ta kafa dokar kulle bane sai dai ya ce gwamnatin jihar a shirye take ta yi duk wani abu mai yuwuwa wajen ceton rayuka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here