Duk da Rashin Nasara a Kotu, Tsagin Aminu Wali na PDP Ya Dakatar da Kwankwaso

0
237

Tsagin jam’iyyar PDP bangaren Aminu Wali a Kano ya dakatar da Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da magoya bayansa daga jam’iyyar.

Sabbin shugabannin tsagin jam’iyyar ne suka dauki matakin, inda suka zargi Kwankwaso da mamaye shugabancin jam”iyyar da kuma kin biyayya ga jam’iyyar.

A wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban tsagin, Muhammad B Lamido, ya soki Kwankwaso da tilastawa Hon. Ali Datti Yako barin jam’iyyar.

Sannan ya soki Kwankwaso da aikata wasu laifuka da suka hada da “rashin da’a, rashin biyayya da kuma rashin girmama dattawan jam’iyya a jihar”.

Sannan ya soki Kwankwaso da karya kundin tsarin mulkin jam’iyyar.

A yan kwanakin nan dai, shugabancin jam’iyyar PDP na kasa ya sanya idanu kan zaben shugabannin jam’iyyar wanda tsagin Kwankwasiyya ya lashe dukkan matakai a Kano wand hakan yasa tsagin Aminu Wali gudanar da nasu zaben daban.

Ko a kwanaki ma sai da kotu ta kori karar da tsagin Aminu Wali ya shigar yana kalunbalantar kwamitin riko na jam’iyyar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here