Akanta-Janar: Al’ummar Garin Gezawa Sun Mayar Wa Da Kungiyoyin ASUU Da Kwadago Martani

0
103

Kungiyoyin ci gaban al’umma dake karamar hukumar Gezawa a jihar Kano, mahaifar Babban Akanta Janar na Najeriya, Alhaji Ahmed Idris sun mayar da martani ga kungiyar malaman jami’o’i ta ASUU bisa kiran da kungiyar ta yi ga shugaban kasa Buhari kan ya sauke babban Akanta Janar din na kasa.

A wata sanarwa da aka rabawa kafafen yada labarai a Kano wacce ke dauke da sa hannun Galadiman Gezawa, Alhaji Lawan Badamasi a madadin kungiyoyin dake karamar hukumar, sun bayyana rashin jin dadinsu ga ikirarin kungiyar ASUU.

Sanarwar ta bayyana cewa, an ja hankalinta kan wata sanarwa ta taba alfaramar Alhaji Ahmed Idris, Akanta Janar na kasa wanda Ko’odinetan Kungiyar ASUU na Jihar Bauchi, Farfesa Lawal Abubakar, ya yi inda ya nemi Akanta Janar din ya yi bayani kan yadda ya mallaki dukiyarsa a Kano.

Sanarwar ta kara da cewa, yin shiru da uwar kungiyar ta ASUU na kasa ta yi kan sukar da Ko’odinetan na Bauchi ya yi na nufin goyan baya ga abin.

“Akwai ingantattun bayanai kan Alhaji Ahmed Idris da danginsa kuma ba zai zama abun mamaki ba ga kowa yaji cewa kafin nadin Ahmed Idris yana daga cikin masu yin harkokin kasuwanci da suka hada da: Noma, Kasuwanci na kayayyakin aikin gona.

“A bayyana yake, babu wata al’umma da za ta rufe kunnenta ko ta zura ido, yayin da ake yiwa danta rashin adalci, don haka muna kalubalantar ku. Muna jiran ganin sakon barranta kai daga kungiyar ASUU reshen Arewa maso gabas don ta nisanta kanta da wannan kalaman na Ko’odinetan shiyya”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here