Ɗaya daga Cikin Gwamnonin Arewa Maso Yamma na Ɗaukar Nauyin Ayyukan Ƴan Bindiga a Yankin – APC

0
331

Jam’iyyar APC ta soki wani gwamna da ba a bayyana sunanshi ba da daukar nauyin ayyukan yan bindiga a kasarnan.

Ba tare da bayyana gamman ba ko jam’iyyar sa, APC a sanarwar da ta fitar a yau Alhamis ta yi ikirarin cewa “Rahotan Binciken sirri” ya nuna wani gwamna daga Arewa maso yamma na hada kai da masu aikata laifuka don tayar da tarzoma a yankin.

Zargin da APC ta yi na zuwa ne bayan da mayakan Boko Haram suka sace dalibai a jihar Katsina dake Arewa maso yamma.

Yankin Arewa maso yamma dai ya hada jihohin Jigawa, Kaduna, Kano, Katsina, Kebbi, Sokoto da jihar Zamfara.

APC na rike da jihohi 5 yayin da PDP ke rike da Zamfara da Sokoto.

“Jami’an tsaronmu suna da rahoton binciken sirri da yake alakanta daya daga cikin gwamnonin Arewa maso yamma na hada kai da yan yan bindiga wajen daukar nauyin yan ta’adda a yankin. Bazan yi karin bayani kan lamarin ba saboda batu ne na tsaro.

“Haka kuma, hukumomin tsaro ya kamata su binciki al’amarin da gaggawa”, cewar mataimakin mai magana da yawun APC, Yekini Nabena.

Jam’iyyar ta kuma zargi PDP da sanya Siyasa kan matsalolin tsaro.

Sannan jam’iyyar ta yi kira ga jami’an tsaro su kasance cikin shiri kuma su tabbatar da an kubutar da daliban makarantar Sakandire ta garin Kankara da aka sace.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here