Siyasar Kano: An Ja Zare Tsakanin Ganduje Da Sha’aban

0
347

Gwamnatin jihar Kano ta yi martani kan wani Bidiyo da ke nuna Hon. Sha’aban Sharada, dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar birni a majalisar tarayya na sukar gwamna Ganduje.

Yayin da yake martani kan Bidiyon wanda ke yawo a kafafen sadarwa na zamani, mai taimakawa Ganduje kan sabbin kafafen yada labarai, Abubakar Aminu Ibrahim ya bayyana Sha’aban sharada wanda shi ne shugaban kwamitin tsaro na majalisar wakilai, a matsayin wanda ya yi kankanta ya ja da Ganduje.

“Sha’aban Ibrahim Sharada, kayi kankanta kayi ja in ja da gwamna. Sai dai masu gidanka wadanda ke goyama baya”, ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Bidiyon sha’aban sharada dai ya bayyana a kafafen sadarwa a yau Laraba, inda yake sukar Ganduje bisa siyar da kadarorin gwamnati.

A Bidiyon wanda Jaridar Prime Time News ta samu ya nuna Sha’aban na fadin cewa a shirye yake kuma ” duk wanda ya raga masa baya kaunar Allah”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here