Farin Ciki Ya Ɓarke A Garin Seme Bayan Umarnin Buhari na Buɗe Boda

0
327

Mintuna kadan bayan umarnin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayar na bude iyakokin Najeriya, al’ummar dake rayuwa a Bodar Seme sun  fara murna don nuna farin cikinsu.

Mazauna yankin sun fara murna tare da babura, inda suke watsa ruwa a jikinsu don farin ciki da jin labarin iyakar.

Najeriya dai ta rufe iyakokinta tun shekarar 2019 don hana shigowa da makamai da kwayoyi.

Ministar Kudi da kasafi, Zainab Ahmed ce ta sanar da umarnin shugaban kasar a yau jim kadan bayan zaman majalisar zartarwa na kasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here