Buhari Na Da Cutar Mantuwa Don Haka Dole Ya Bar Mulki – Junaid Mohammed

0
861

Tsohon dan majalisa a jamhuriya ta biyu kuma dattijo a arewacin Najeriya, Dr. Junaid Mohammed, ya ce yakamata shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi murabus saboda bazai iya tafikar da lamuran da suka shafe shi ba ma balle na mutane miliya 200.

Junaid Mohammed ya shaidawa jaridar Sahara Reporters cewa shugaba Buhari bai da isasshiyar lafiyar da zai jagoranci kasa kamar Najeriya.

Ya kuma soki masu taimakawa shugaban kasar bisa boye ainihin lafiyar shugaban kasa.

Da yake magana kan matsalar rashin tsaro ya ce, “Kasancewa shugaban kasa, bashi da wani hakki na yiwa yan kasa ba dai-dai ba. Idan bashi da lafiya, yan Najeriya na bukatar sani. Idan ba zai iya gudanar da aikinsa ba , ya kamata a sanar da mutane.”

Dattijan ya kuma yi ikirarin cewa, shugaba Buhari yana da matsalar mantuwa don haka bazai iya ci gaba da gudanar da mulkin kasarnan ba.

“Ya kamata a bukaci ya sauka daga mulki”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here