Ɗaliban Sakandire Da aka Sace a Katsina Suna Wani Daji a Zamfara – Masari

0
99

Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari ya ce, daliban makarantar Sakandire ta Kankara da aka sace ranar Juma’a da ta gaba suna wani daji a jihar Zamfara.

Masari wanda yake amsa tambayoyi a shirin gidan Rediyon BBC na dare a yau Laraba ya ce ya samu bayanai cewa daliban na jihar Zamfara.

“Suna dajin Zamfara, mun samu labari”, inji Masari.

Ya ce gwamnatinsa na tattaunawa da masu garkuwa da mutanen don tabbatar da an saki daliban.

Masari ya yi bayanin cewa, ya fara tattaunawa da masu garkuwa da daliban, inda ya tabbatar da cewa, gwamnatinsa za ta ceto daliban.

” Muna tattaunawa da wadanda suka sace daliban kuma muna son tabbatar da cewa an sake su”, inji shi.

Sannan kuma ya karyata batun cewa kungiyar Boko Haram ce ta sace daliban.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here