Ɗaliban Kwalejin Ilimi ta Sa’adatu Rimi na Zanga-Zanga Kan Rufe Makarantu a Kano

0
195

Daliban kwalejin ilimi ta Sa’adu Rimi dake Kano sun rufe titin Zaria inda suke zanga-zanga kan rufe makarantu da gwamnatin jihar ta yi.

Daliban na zanga-zanga ne don nuna bacin ransu kan sanarwar rufe makarantu, inda suka rufe hanya don nuna kin amince da matakin.

Gwamnatin jihar Kano dai ba ta yi karin hasken kan musabbabin rufe makarantun ba.

Jaridar Sahelian Times ta rawaito cewa, rufe makarantun na da alaka da matsalar tsaro.

 

Akwai karin bayani nan gaba….

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here