Yanzu-Yanzu: Matar El-Rufai da Ɗansa Sun Kamu da Cutar Korona

0
271

Daya daga cikin matan gwamnan jihar Kaduna, Hajiya Ummi El-Rufai tare da dansa, Bahsir El-Rufai sun kamu da cutar Korona.

Jaridar Sahelian Times ta rawaito cewa, Bashir tare da matarsa suna kan hanyarsu ta fita daga kasarnan, bayan daurin auren su yayin da sakamako ya nuna suna da dauke da cutar.

Matar gwamanan, Hajiya Ummi wacce ita ma ta kamu da cutar an gano tayi mu’ammala da mutane biyar.

Wata majiya ta shaida cewa, hudu daga cikin mutanen da matar gwamnan tayi mu’ammala da su sun kamu da cutar.

Tun a ranar Lahadi ne dai, Nasir El-Rufai ya kilkace kansa bayan gano cewa wasu daga iyalansa sun kamu da cutar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here